<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><hymn_number>575</hymn_number>
<title>Yesu Mai Ceto, Lalle Shi Ne Mai Cetonmu LW575</title>
<lyrics>[V1]
 Yesu Mai Ceto, lalle shi ne mai cetonmu
 Muna murna murna mai yawa za mu yi,
 Domin Yesu ya mutu domin laifinmu.
 Ya mutane. ku tuba, ku tuba,
 Ku tuba, ku bi Yesu.
 Kada ku zamna a cikin zunubanku.
 Ku zo yanzu, ku tuba, ku bi Yesu.
 Ba wata hanya do za mu sami ceto
 Ba wani Allah a cikin wannan duniya,
 Da ya iya ya wanke zunubanmu.
 Sai Yesu kaɗai, Ɗan Allah mai iko duka,
 Shi ne ya zo, ya mutu domin laifinmu
 Shi mai rai ne, ya tashi, ya tashi,
 Ya tashi daga kabari.
 Ya hau sama, yana shirya mana wuri.
 Wata rana za mu je, za mu je,
 Za mu je gidan Allah.
 Za mu raira waƙoƙi na yabonsa
 Mu ce masa, halleluya, halleluya,
 Za mu ce masa, halleluya, Amin.</lyrics>
</song>